Wednesday, October 16, 2019

Banban kuskuren Dana tafka a gidan mijina!!


_Kashi na 4 (part 4)_
*BABBAN KUSKURAN DA NA TAFKA A GIDAN
MIJINA*
_Daga shafin ma'asumiyya News updates_
*Tare da dan uwan ku Habib Rabiu Nasrallah.*
_Da farko ina neman gafara sakamakon jin kirin da
aka samu na cikaban wannan labari, sakamakon,
Wasu manyan dalili, kamar rasuwar kanwata, da
kuma Rashin da yasameni na rashin yan uwa da
abokan Arziki fatana Allah ya karbi uzurinsu_.
_Baya ga haka ina godia da sakonnin ku da ku ke
turowa ta email ina godia Allah ya bar zuminci_.
*A rubutun mu na baya mun tsaya gun da khalisat
ta na cikin daka yajin awara a tsakar gidan, a yayin
da gidan ya turnike da yaji, mahaifiyar ta na fada,
domin ta shiga hakkin su, ta rufeta da fada, haka
taje ta dakko kofin ruwa domin ta yayyafa, domin
samun saukin yajin, katsaham sai ta ji, sallamar
wani yaro dan unguwar su, me suna Abubakar ya
shigo, ya nufo gunta da takarda ya ce da ita gashi
inji Mubarak Anan na tsaya zan dora.*
Nan ta ke cikin sauri na ajiye kofin da ke hannun,
bansan lokacin da na nemi tarin da na ke yi akai-
akai ba, sakamakon yajin da na ke da kawa, cikin
sauri na karbi takarda, daga hannun Abubakar don
naga me ke cikinta. Yaran ya na bani bai bata
lokaciba, ya juya, da Alama hankalin sa ya na kan
wasa, domin ya na yin sa, tamakar akwai abin da ya
ke aka aiko shi, baya ga haka, sakamakon rana ta
take babu kowa a tsakar gida kannena da
mahaifiyata, da kishiyarta duk su na cikin daki.
Batare da bata lokaciba, na bude wasikar cikin
azama sai naga rubutu, kamar haka.
_Bayan sallama da dukkan girmamawa khalisat.
Batare da bata lokaciba, khalisat na san da cewar
kin dauki tsawan lokaci, ki na bukatar na sauwake,
miki, duba da yadda, na fahimci Arzikin da Allah ya
bani, ko na ce dukiyar da Allah ya bani ya karbe
abinsa, wanda wannan ba kaina farauba, ba kuma
karauba. Tare da cewar nasan jarrabawa ce amman
wani abin bakin ciki wanda a rayiwata bazan taba
mantawaba, banyi kuma zatan hakan zai faru
gareniba, shi ne ta yadda ki kanunamin, ki na zaune
da ni sabo da dukiyata, duk soyayyar da ki ke
nunamin badomin Albaya badomin Allah ba ne, a
haka na hakura, na cigaba da zama da ke. Shakka
babu kin san halin da na shiga daga dan gina
domin ki, amman na kafe, sai ke, wanda su suna
ganin ke ba yar masu da shiba ne, ni kuma nasan
da cewa arziki na Allah ne, shi ke ba dashi, amman
gabadaya karshe ki karinka azabtar dani, badan
komaiba domin dukiyar da na mallaka Allah (T) ya
karbi abinsa_.
_Sabo da haka khalisat Allah ya sani na soki domin
Allah na kula da ke na sauke duk wani nauyi da ke
kaina, badan komai ba don na faran tamiki, na yi
miki uziri wanda bansan adadiba, sakamakon haka
kin bikaci na sauwake miki tun a baya domin kin ce
ba zaki iya rayiwa da ni cikin talauciba. Sabo da
haka ina rokan Allah ya baki wanda ya fini, dokiya
da hakuri, da juria da duk kan abin da ki ke bukata,
Allah ya baki. Fatana Idan Lokacin daurin Auren ki
ya zo, ina xuba ido da ganin katin gayyata, kuma
inshaAllah zanzo, zan kuma ta ya ki da addua. Sabo
da haka._ *NI MUBARAK NA SAUWAKEWA
KHALISAT MUSA, ABISA IGIYA UKU.*
AKARSHE INA ADDUAR ALLAH YA BA KI MIJI
WANDA YA FINI, HAZA BISSALAM KI HUTA LAFIYA.
Daga uban yayan ki Mubarak S. Adam.
Da kammala karatun ta kardannan ban san, lokacin
da na yanke jiki na, fadi kasa ba, sakamakon
tsananin bacin rai, su dai cikin gida sai ji sukai
anfadi, kishiyar ta mahaifiya haka ta nufo guna da
guda ta na cewa lfy, haka itama mahaifiyata haka ta
fito da gudu, da sauran kannena, wasu daga ciki
suna kuka, ita kanta mahaifiyata banda innali... Ba
abin da take cewa, tun daga nan ban san inda kaina
ya ke ba, sai sai farkawa na yi naganni a gadan
asibibiti, mahaifiyata ta na gefena ta ci kuka ta
godewa Allah idon ta, gabadaya ya sauya ya yi
jajawur, wanda bantaba sanin ta na sona, sai a
wannan ranar, farfadowa ke da wuya, maman mu
cewa ta ke khalisat, sannu.
Bayan wasu kwanika haka aka sallamomu, wanda
na ci kuka nagodewa Allah, domin abu biyu na ke
tunani, wlh nasan na zalinci mubarak matsananci
zalinta, wanda nasan da cewa har abada idan har
bai ya femin ba, nashiga uku, Tabbas zai yi wahala
na mayar da miji kamarsa, har abada. Tabbas
soyayya Ta Allah da Annabi ita ce soyayya badan
kwadayin abin duniya.
A kwana a tashi, wata da watannin,bayan na yi idda,
kulin ina cikin damuwa, gashi Allah ya jarabceni da
son mubarak kamar kamar me. ga shi farin jinin da
na ke takama da shi, ta kai ya ragu 80 bisa dari,
gashi ina mutukar san na yi auran, amman kashi
ashirin cikin dari, daga ka ce mutum ya fito sai ya
gudu. Wanda zaman da na ke acikin gidan mu, sai
da takai ko da wanda bashi da abin da xaici sai ya
fita ya nemo, ya aureni zaifimin kwanciyar hankali.
akwana atashi sai da na yi shekara uku da wata 8 a
gidan mu, dakyar nasa miji shima sai da rokan
Allah, gashi yana da mata uku, duk da cewa akallah
zai kai 43-45 haka dole na amenta aka kaini wanda
uhmm... Rayiwar gidan ba acewa komai.
Allah cikin ikonsa mubarak ya sami aiki a CBN ta
sanadiyar mahaifin wacce ya aura, gabadaya kusa
rayiwar sa, ta koma Abuja, haka zalika matar da Ya
aura ma'akaciyar bakin ce babba.
Hakika a rayiwata bantaba da nasaniba kamar
wannan tabbas hausawa na cewa da nasani ke ya
ce.
Kirana ga yan uwan mata ki yi kokarin rokan Allah
Ya baki miji nagari kar ki yarda ki so mutum domin
Abin hannunsa, Tabbas na yi da na sani a rayiwata,
mutuka.
A karshe ina kira ga duk wacce take da wannan
dabi'ar irin tawa ta dauki darasi daga gare ni,
Tabbas rayiwar duniya abar tsoroce madamar baka
shin fida rayiwar ki, abisa umarnin Allah da haninsa
ba.
*Daga khalisat Musa*
*Rubutawa Habib Rabiu Nasrallah*

Email:Habibrabiu81@gmail.Com

Monday, January 7, 2019

Garabasa

Tuesday, January 1, 2019

ASUU Update.

ASUU is going to call up the on the ongoing indefinite strike on Monday 7th Jan. 2019.